Iyalan tsohon shugaban kasa na mulkin soji marigayi Sani Abacha, sun fara kare martabar mahaifin su bayan kalaman tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida Babangida, da yace Abacha ne ya rika kitsa yanda za’a kifar da gwamnatin sa ta hanyar tarzoma.
Daya daga cikin yayan Abacha, mai suna Sadiq S. Abacha, yace mahaifin nasu ya taka muhimmiyar rawa a mulkin Najeriya, kuma har yanzu ana amfanar ayyukan sa.
Idan za’a iya tunawa a ranar Alhamis data gabata ne aka gudanar da taron kaddamar littafin rayuwar Babangida, wanda a nan ne yace Marigayi Sani Abacha, ya rika kulla hanyoyin da za’a kifar da Gwamnatin sa.
Sadiq, yayi bayani a kafar sada zumunta inda yace tarihi ba zai manta irin gudunmuwar da Abacha ya bawa kasar nan ba.