Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, yace akwai bukatar a yabawa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, bisa rawar daya taka a fannin inganta tattalin arzikin Najeriya a zamanin mulkin Obasanjo.
El-Rufa’i, ya bayyana hakan a lokacin da yakai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Edwin Clark, dattijon Neja Delta, wanda ya rasu a ranar 17 ga watan Fabrairu.
El-Rufa’i, yace babu wanda yake yabawa Atiku Abubakar, dangane da rawar daya taka wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya a lokacin da yake matsayin mataimakin shugaban kasa a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007.
Tsohon gwamnan na Kaduna yace rashin rubuta kokarin da Atiku yayi a baya shine yasa har yanzu mafi yawancin mutane basu fahimci alkairin daya samar ba.
Sai dai idan za’a iya tunawa a shekarar 2016, El-Rufa’i ya zargi Atiku Abubakar, da yada karya da kuma goyon bayan cin hanci da rashawa.