Majalisar wakilai ta nemi a samar da sansanin sojoji a yankin Bukuyum na jihar Zamfara biyo bayan karuwar lalacewar tsaro a yankin.
Ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Bukuyum, Sulaiman Abubakar Gumi, ne ya gabatar da ƙudirin, inda ya ce ƴan bindiga sun mayar da yankin wata mafaka.
Gumi, yace fatattakar yan ta’adda da ake yi a Shinkafi ne yasa suke guduwa zuwa yankin Bukuyum.
Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin arewa masu fama da tabarbarewar sha’anin tsaro.