Kwankwaso yace NNPP zata iya kwace mulkin Najeriya a hannun APC

0
140
Rabiu-Musa-Kwankwaso-
Rabiu-Musa-Kwankwaso-

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, yace inde za’a yi sahihin zaɓe jam’iyyar NNPP zata iya karbar mulkin Najeriya a shekarar 2027.

Kwankwaso yace jam’iyyar NNPP za ta kayar da dukkan jam’iyyun siyasa ta hanyar yin zabe mai inganci da adalci.

Kwankwaso ya bayyana hakan a ranar Alhamis a lokacin daya halarci taron kwamitin zartarwa na NNPP a matakin kasa daya gudana a Abuja.

Dan takarar shugabancin kasar na NNPP a zaben 2023 ya soki gwamnatin Bola Tinubu, inda yace yan kasa sun shiga kuncin rayuwa a karkashin mulkin sa.

Ɗan takarar yace da wuya a samu wani mutum dake yin farin ciki da jam’iyyar APC musamman daga matakin kasa.

Sannan yace an rasa tsaro a karkashin APC, an rasa ababen more rayuwa, tare da samun yaduwar talauci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here