Rikicin majalisar dokokin jihar Lagos ya zama sabo

0
45

Kakakin majalisar dokokin jihar Lagos da aka tsige Mudashiru Obasa, yayi watsi da zargin da aka yi masa na cewa an gano maboyar makamai a ofishin sa.

Bayanin Obasa, ya fito a jiya Laraba, sakamakon cigaba da fuskantar rikicin majalisar bayan sanar da tsige shi tare da zabar Mojisola Meranda, a matsayin sabuwar shugabar majalisar, a kwanakin baya.

Haka zalika, itama Mojisola Meranda, ta karyata labarin cewa ta sauka daga mukamin kakakin majalisar, a daidai lokacin da majalisar ta sake yin watsi da zargin cewa wasu mambobin ta su 27 na shirin ficewa daga APC zuwa LP.

Cikin wata sanarwa da Obasa, ya sanyawa hannu yace zargin sa da mallakar makamai wata karya ce babba da aka shirya.

Idan za’a iya tunawa yau kwanaki uku kenan bayan da jami’an tsaron farin kaya DSS, suka mamaye majalisar dokokin jihar Lagos, inda suka rufe ofishin kakakin majalisar, da hana yan majalisar zama kamar yadda suka saba, duk da cewa daga baya majalisar ta zauna karkashin jagorancin Mojisola Meranda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here