Rikici ya barke a zauren majalisar dattawa

0
113

Rikici ya kaure a majalisar dattawa lokacin da shugaban majalisar Godswill Akpabio, ya nemi Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta fice daga zauren majalisar.

Natasha, wadda yar majalisa ce daga jihar Kogi, taki ki ficewa daga majalisar tare da cewa ko kadan bata tsoron Akpabio, kuma ba zata yi shiru ba.

Tun da farko an fara yin takaddama akan sauyawa Natasha wajen zama a majalisa ba tare da sanin ta ba, wanda hakan yasa ta tambayi shin mene ne yasa aka canja wajen zaman ta ba’a sanar da ita ba.

Daga bisani komai ya daidaita tare da cigaba da gudanar da zaman majalisar na yau Alhamis.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here