Jam’iyyar NNPP, tayi rashin dan majalisar wakilai Yusuf Galambi, wanda ya koma jam’yyar APC mai mulkin kasa.
Dan majalisar ya sanar da ficewar sa a yau Alhamis, cikin wata wasikar daya aikewa kakakin majalisar wakilai Tajuddeen Abbas, sannan aka karanto ta a yiayin zaman majalisar na yau.
:::Saukin farashin fulawa ba zai sa mu rage farashi ba—Kungiyar masu gasa Burodi ta Kano
Galambi, shine ke wakilar mazabar Gwaram, ta jihar Jigawa a majalisar wakilai ta 10.
Dan majalisar yace al’ummar mazabar sa ne suka nemi ya fice daga NNPP, tare da koawa APC, a cewar sa rikici ya mamaye tsohuwar jam’yyar tasa.