Gwamnatin Amurka ta musanta daukar nauyin ayyukan kungiyar Boko Haram da sauran yan ta’addan Najeriya, inda tace babu wata hujjar da za’a bayyana akan zargin.
Jakadan Amurka a Kasar nan Richard Mill, ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai, kan zargin da daya daga cikin yan majalisar dokokin Amurka yayi inda yace kungiyar Boko Haram, tana samun taimako daga hukumar USAID ta Amurka, har ma da taimakawa sauran wasu kungiyoyin yan ta’adda.
Richard Mills, yace Amurka tana daukar tsauraran matakan da ba za’a iya karkatar da kudaden tallafin hukumar USAID, zuwa ga hannun yan ta’adda ba.
Jakadan ya zanta da manema labaran ne a birnin tarayya Abuja, bayan tattaunawa da Kungiyar gwamnonin Najeriya a cikin daren Laraba, inda yace babu wata kasa a duniya da take yin ala wadai da ayyukan Boko Haram kamar Amurka.
Idan za’a iya tunawa a ranar 13 ga watan Fabrairu ne dan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Republican Scott Perry, ya zargi USAID da tallafawa kungiyoyin yan ta’adda cikin su har da Boko Haram.
Tuni dai majalisar dattawa ta gayyaci mai bawa Shugaban Kasa shawara akan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da sauran manyan jami’an tsaro don yin bayani akan zargin.