Tsohon shugaban kasa na mulkin soji Janar Ibrahim Badamasi Babangida, mai ritaya yace Moshood Abiola, ne ya lashe zaben shugaban Najeriya da aka gudanar ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993.
Janar Babangida ya bayyana hakan ne a cikin littafin tarihin rayuwarsa mai suna “A Journey in Service” wanda aka kaddamar a Abuja a yau Alhamis.
:::Kisan dalibai 5 ya janyo rufe jami’ar tarayya dake Lokoja
Ta bakin mai bitar littafin kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo, Babangida ya bayyana cewa, Marigayi MKO Abiola, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), shine ya lashe zaben shugabancin Najeriya a 1993, bisa samun rinjayen kuri’un al’umma.
Babangida ya bayyana soke zaben na ranar 12 ga watan Yuni a matsayin abu mafi fuskantar kalubale a rayuwarsa.
Ya kara da cewa babu shakka Abiola, ne ya lashe zaben kuma ya cika duk wasu sharudan zama shugaban kasa a wancan lokaci.