Abacha yaso kifar da gwamnatina ta hanyar tarzoma—Babangida

0
93

Tsohon shugaban kasa na mulkin soji Ibrahim Badamasi Babangida, yace Janar Sani Abacha, yayi yunkurin kifar da Gwamnatin sa ta hanyar yin amfani da tarzoma.

Babangida ya sanar da hakan a yau lokacin da yake yin jawabi a wajen taron kaddamar da littafin rayuwar sa a Abuja.

Taron ya samu halartar daukacin tsaffin shugabannin Najeriya, sai tsohon shugaban kasa Buhari, daya turo wakilcin sa.

Shima tsohon shugaban kasar Ghana Nana Akufo Ado, ya halarci taron.

Manyan yan siyasar Najeriya da attajirai ma sun zo taron, cikin su har da Alhaji Aliko Dangote da da Abdulsamad Isyaka Rabi’u, wanda suka yi alkawarin bayar da tallafin Naira biliyan 13, ga dakin karatun da Babangida ya Gina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here