Wani ya kashe abokin sa bayan hada masa liyafar abinci

0
33

Ana zargin wani mutum mai suna Iliyasu Mohammed ya kashe abokin sa Saifullahi Muhammad, da adda bayan Iliyasu ya gayyace Saifullahi cin liyafar abinci.

Ana zargin Iliyasu ya kashe abokin nasa bayan kammala cin abincin daya bashi a kauyen Dantata dake birnin Abuja.

:::Jamhuriyar Nijar ta hana ‘yan Najeriya shiga kasar

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Abuja Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar hakan cikin wata sanarwar data fitar a yau Laraba.

Tace sun samu labarin kisan a ranar 13, ga watan Fabrairu, inda jami’an su suka iske Saifullahi a cikin jini sannan a kusa dashi an samu adda da ake zaton da ita Iliyasu yayi amfani wajen aikata kisan.

Adeh, yace sun kama wanda ake zargi da kisan dan kimanin shekaru 23, kuma ana gudanar da bincike akan sa, dangane da aikata kisan kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here