Shalkwatar tsaron kasa ta yaye tsaffin mayakan Boko Haram

0
36

Shalkwatar tsaron kasa ta kammala gyara halayen yan ta’adda 789, da suka mika wuya ga jami’an tsaro.

:::Murar tsintsaye ta kashe kaji 300, a gidajen gona

Rundunar tace tsaffin yan ta’addan sun hadar da yan Boko Haram, da masu aiki a sauran kungiyoyin bata gari, wanda tuni aka mayar dasu cikin al’umma don cigaba da yin rayuwa kamar sauran mutane.

Babban hafsan tsaron kasa Janar Christopher Musa, ne ya bayyana hakan inda yace tsaffin mayakan 381, sun koma cikin yan uwan su bayan zaman gyaran hali a hannun gwamnati.

Musa, ya bayyana hakan ta bakin shugaban sashin tsare-tsare na shalkwatar tsaron AVM Sayo Olatunde, lokacin da aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki a birnin tarayya Abuja ranar Talata.

Hafsan tsaron, ya kara da cewa tsaffin mayaka 120,000 da iyalan su sun mika wuya tare da zubar da makaman su, wanda yanzu an yaye 789, daga cikin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here