Murar tsintsaye ta kashe kaji 300, a gidajen gona

0
24

Cutar Murar tsintsaye ta kashe kaji 300, a gidajen gonar jihar Filato.

Babban likitan dabbobin jihar Dr Shase’et Sipak, ne ya bayyana hakan a yau Laraba, lokacin da yake yin jawabi ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, akan barkewar cutar a birnin Jos.

Yace cibiyar bincike akan lafiyar dabbobi ta kasa NVRI, dake Jos ce ta gano barkewar cutar.

Ya kara ce cewa gidajen gonar da aka samu barkewar murar tsintsayen sun kasance a karamar hukumar Bassa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here