Sheikh muhammad bin usman, zai cigaba da yin limanci a tsohon masallacin sahaba.
Shugaban majalisar malamai ta jihar kano, malam ibrahim khalil, ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Yace sun zanta da kowanne bangare dake takaddama akan masallacin jami’ur rahman, kuma an yanke hukuncin cigaban limancin sheikh muhammad bin usman, a tsohon sahaba, yayin da ay mai kifi, da mukarraban sa zasu cigaba da tafiyar da al’amuran masallacin jami’ur rahman.
Malam Ibrahim Khalil, yace Sheikh Muhammad Bin Usman, ya amince zai koma tsohon Masallacin Sahaba dake kundila don cigaba da al’amuran sa.
Shugaban majalisar malaman ya godewa jami’an tsaro bisa gudunmuwar da suka bayar yayin rikicin Masallacin wanda haka yasa ba’a samu tashin hankali ba.