Gwamnatin Kano zata biya ma’aikatan shara albashin watanni 9

0
74

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirin biyan ma’aikatan shara hakkin su na albashin watanni 9 da suke bin gwamnatin bashi.

Akalla ma’aikata 2,369, ne ke yin aiki tsawon wadancan watanni ba tare da biyan su hakkin su ba, inda za’a biya albashin daga watan Yuni na shekarar 2024, zuwa Fabrairun 2025.

:::Dangote ya zama mutum na 86, a cikin masu kudin duniya

Kwamishinan ma’aikatar muhalli ta jihar Dahiru Hashim, ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Kano.

A cewar kwamishinan yin hakan zai kara karfin gwuiwar ma’aikatan wajen kula da aikin su da kuma tsaftace jihar.

Dahiru, yace dole a yabawa ma’aikatan saboda juriyar da suka nuna wajen yin aikin watanni 9, ba tare da samun hakkin su ba, yana mai cewa nan gaba kadan za’a fara tantance su don biyan su albashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here