Gwamnan Adamawa ya soke nadin sarautar sa dana Atiku Abubakar

0
353

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya soke nadin sarautar gargajiyar da akayi masa da kuma wanda aka yiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Boni Haruna, da karin wasu mutane.

Kafin yanzu mutanen uku suna rike da sarautun Sarkin yakin Mubi, Wazirin Adamawa da Makaman Mubi.

Hakan ya biyo bayan kirkiro wasu sabbin masarautu a jihar ta Adamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here