An roki shugaban kasa Tinubu ya daidaita darajar HND da Digiri

0
38

Kungiyar kwalejojin kimiyya da fasaha masu zaman kansu ta kasa ta roki shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya dauki nauyin gabatar da kudirin cire banbancin dake tsakanin darajar kwalin kammala karatun Digiri da kuma babbar Diploma (HND).

:::An Kaiwa Musulman Burtaniya harin da basu taɓa fuskanta ba a shekarar 2024

Shugaban kungiyar Dr Benjamin Achiatar, ne ya nemi hakan a yau lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Abuja, ranar laraba.

NAN, ya rawaito cewa banbancin dake tsakanin masu HND da masu digiri na sakawa a nunawa masu shaidar kamamala HND, banbanci a guraren ayyukan gwamnati.

Achiatar, yace duk da a baya an sanar da cewa an janye banbancin dake tsakanin HND da digiri, amma ba’a aiwatar da daidaita darajar karatun a guraren aikin gwamnati ba, saboda ba’a kafa doka kan hakan ba.

Shugaban kungiyar kwalejojin masu zaman kansu, yace majalisa ta 9, ta yi dokar daidaita darajar HND da Digiri amma shugaban kasa bai sanyawa dokar hannu ba, wannan ne yasa akwai bukatar a sake bibiyar kudurin ko a samar da sabon kudirin da zai daidaita darajar kwalayen biyu a majalisa ta 10.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here