An samu karuwar nunawa mabiya addinin muslinci tsana da kai musu hari a Burtaniya
An bayyana cewa mabiya addinin muslinci na cigaba da fuskantar tsana da kyamar da basu taɓa fuskanta ba a kasar Burtaniya.
Wata kungiyar dake sanya idanu dangane da yawan farmakin da ake kaiwa mabiya addinin muslinci a kasar Burtaniya da kuma tantance harin mai suna Tell Mama, itace ta bayyana hakan, bisa cewa hakan ya faru a shekarar data gabata 2024, inda aka kaiwa musulmai harin da ba’a taba samun adadin sa a baya ba.
Tell Mama, tace a 2024, an kaiwa musulmai hare haren da yawan su yakai 6,000, saboda a nuna musu kyama da tsana.
Bisa bayanan kungiyar hakan baya rasa nasaba da yaɗa kalaman ƙarya da ke bayyana Musulmai a matsayin ‘yan ta’adda ko kuma masu goyon bayan ‘yan ta’adda.
Musulmai maza sune suka fi fuskantar harin da kyama, inji Tell Mama.