
Kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon kafa ta Spaniya ya dakatar da Jude Bellingham na Real Madrid wasanni biyu a yau Laraba, bayan da aka kore shi daga wasan da suka buga da kungiyar Osasuna, a ranar Asabar data gabata.
:::An Kaiwa Musulman Burtaniya harin da basu taɓa fuskanta ba a shekarar 2024
Ana zargin cewa an kori Bellingham, daga wasa bayan yayi kalaman tunziri ga alkalin wasa Jose Munuera Montero, wanda haka ne yasa aka bashi jan kati.
Jose Munuera Montero ya kori dan wasan na Ingila a lokacin da Madrid ta buga wasan da aka tashi 1-1 a tsakanin ta da Osasuna.
Bellingham, dai ya kafe akan cewa bai zagi alkalin wasa a yayin wasan su da Osasuna ba, kuma duk da haka ba zai samu damar buga wasannin da Madrid zata yi da kungiyoyin Girona da Real Betis ba a ranar 23 ga Fabrairu da 2 ga watan Maris.