Za’a ci tarar Naira 300,000 ga masu yin cuta a Mitar wutar lantarki

0
63

Hukumar kayyade farashin wutar lantarki (NERC) tace daga yanzu masu yin cuta a mitar wutar lantarki zasu rika biyan tarar naira dubu dari 2, da kuma dubu dari 3, idan aka same su da aikata wasu laifuka musamman jirkita mitar zuwa shan wuta ba tare da siyan kati ba.

:::Majalisar wakilai na son daukar tsauraran matakai akan masu kashe Mata

Jaridar Guardian ta rawaito cewa daukar matakin ya biyo bayan sabunta dokokin hukumar da akayi dangane da hukunta masu yin cuta wajen yin amfani da mitar lantaki.

Dokar mai lamba NERC/REG/41/2017, ta fara aiki a ranar 22, ga watan Junairun 2025, inda za’a ci tara naira dubu 100,000, ga mai amfani da mita mai layi daya in yayi laifin farko sai dubu 150, a laifin na 2.

Hukuncin ya kuma tanadin biyan tarar naira dubu dari 2, zuwa dubu dari 3, ga wadanda suka aikata laifi a mita mai layi uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here