Jagoran Kungiyar al’ummar kudu maso kudu Edwin Clark, ya mutu.
Clark, ya mutu yana da shekaru 97, a duniya. A baya ya taba rike mukamin kwamishinan yada labarai na gwamnatin tarayya.
Wata sanarwar da daya daga cikin iyalan mamacin mai suna Farfesa C. C. Clark, ya fitar tace Edwin Clark, ya mutu a daren jiya Litinin.
Clark shine shugaban kungiyar al’ummar yankin Neja Delta mai suna (PANDEF).
Rasuwar tasa tazo kwanaki kadan bayan mutuwar jagoran kungiyar Yarabawa ta Afenifere Ayo Adebanjo, wanda ya mutu yana da shekaru 96..