Rikicin zaben kananun hukumomi ya kashe magoya bayan APC da PDP su 8

0
52

Rikicin zaben kananun hukumomi ya kashe mutane 8 a Osun.

Wani kazamin rikicin daya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da PDP, yayi sanadiyyar mutuwar mutane 8 a jihar Osun, a jiya litinin.

Rikicin ya samo asali akan wadanda suke da ikon yin mulkin kananun hukumomin jihar, duk da cewa kotu ta shiga cikin maganar kafin barkewar rikicin, inda ta hana rushe mutanen dake rike da mukamai a kananun hukumomin.

Cikin mutanen da aka kashe lokacin rikicin da aka mamaye daukacin sakatariyar kananun hukumomin jihar akwai jami’an kananun hukumomin da karin wasu mutane.

An bayar da rahoton cewa mutanen sun yi amfani da bindigu a lokacin fadan.

Gwamnatin jihar Osun tace an kashe magoya bayan PDP 5, yayin da APC tace an kashe mata mutane uku.

Dukkanin jam’iyyun suna ikirarin cewa sune ke da ikon rike shugabancin kananun hukumomin jihar, bayan hukuncin da wata kotun tarayya dake Osogbo, ta yanke na dakatar da korar shugabannin kananun hukumomin da kansiloli.

Bayan faruwar lamarin, gwamna Adeleke, ya umarci jami’an tsaro su takawa rikicin birki, kamar yadda ya sanar a shafin sa na X.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Yemisi Opalola, tace zata yi karin haske akan lamarin bayan gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here