Majalisar wakilai ta yi kira ga hukumomin gwamnatin tarayya su rika aiwatar da tsauraran matakai na yaki da ayyukan kashe-kashen mata.
:::Hauhawar farashin kayyakin masarufi ta sauka zuwa kaso 24.48
Dan mmajalisar wakilai na jihar Rivers Awaji-Inombek Abiante, da wasu yan majalisar uku ne suka gabatar da kudirin, a yau talata.
Yace bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasa kowanne dan Najeriya yana da yancin yin rayuwa, sai dai wasu na yiwa ‘ya’ya mata kisan gilla da hakan ke kawo karshen rayuwar su.
Abiante, yace sau da yawa ana kashe mata saboda yanayin jinsin halittar su, kuma hakan yana karuwa a yan shekarun nan.
Kudirin ya nemi majalisar shari’a ta kasa ta tsara samar da wani sashi na musamman a kowanne matakin kotuna wanda zai rika kula da zarge-zargen kisan mata a fadin kasa.