Gwamnatin Katsina ta rabawa mata awaki na Naira biliyan 5.4

0
68

Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda, ya kaddamar da rabon tallafin awakai 3,610 ga matan daukacin kananun hukumomin jihar, inda za’a bawa mata 10 tallafin daga kowacce mazaba.

Radda, ya kaddamar da rabon a jiya litinin inda aka fara da garin Dan-Nakolo, dake karamar hukumar Daura.

Gwamnan yace kaddamar da shirin koyawa mata kiwon dabbobin da kuma tallafa musu ba wai ya tsaya a fannin inganta harkokin noma bane, sai dai zai  sanya gwamnatin ta cika burin ta na zama babbar jihar da take yin kiwo da samar da albarkatun kiwo a fadin arewa, da kasa baki daya.

Yace shirin koyar da kiwon an samar da shi akan kudi naira biliyan 5.7, don taimakawa manoma musamman kungiyoyin mata.

Kowacce mace zata ci gajiyar awakai 4, daga mazabun jihar 361.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here