Bamu fasa gudanar da taron Al-Qur’ani mai girma na kasa ba—Bala Lau

0
47

Shugaban kungiyar Izala na Najeriya Abdullahi Bala Lau, yace suna nan suna cigaba da shirin gudanar da babban taron Al-Qur’ani mai girma na kasa baki daya, wanda aka sanar da dakatarwa.

Bala Lau, ya sanar da hakan ne lokacin da yake zantawa da DW Hausa, inda yace majalisar harkokin addinin muslinci ta Najeriya karkashin jagorancin Sarkin Musulmi ce ta shirya gudanar da taron ba wai kungiyar Izala ba.

Yace tun da farko an tsara cewa mutane 30,000 ne zasu halarci taron, amma daga bisani aka samu mahaddata Al-Qur’ani mai girma, fiye da dubu dari 5, sun nuna sha’awar halartar taron. Yace wannan shine dalilin É—age lokacin taron don samar da ingantaccen tsarin da taron zai gudana ba tare da samun matsalar cunkoson mutane ba.

Bala Lau, yace manufar taron shine a zauna domin tattaunawa a fitar da mafita akan abubuwan da suke damun al’umma da manufar samun hadin kai daga kowanne bangare, ta hanyar yin nazari akan Al-Qur’ani, sakamakon cewa kowa yana da damar bayar da gudunmuwar sa a yayin taron na kasa.

Yace da farko wasu sun saka siyasa a maganar taron amma daga baya sun gane gaskiyar cewa don hadin kan Najeriya aka shirya hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here