An shafe watanni uku ba tare da sanin inda aka kai mataimakin gwamnan jihar Taraba ba

0
100

Ana cigaba da bayyana da damuwa dangane da rashin sanin inda aka kai mataimakin gwamnan jihar Taraba, Aminu Alkali, watanni uku da suka wuce sakamakon fama da rashin lafiyar da yake yi.

Mataimakin gwamnan ya bar jihar Taraba, tun a watan Nuwamba na shekarar 2024, don neman lafiya, sai dai har kawo wannan lokaci gwamnatin jihar bata sanar da al’umma inda Alkali yake ba.

Da farko an samu bayanai dake cewa an kwantar dashi a asibitin tarayya dake Abuja, duk da dai ba’a sanar da rashin lafiyar dake damun sa ba. Wata Majiya tace an fita dashi zuwa kasar Masar biyo bayan tsanani da rashin lafiyar tasa tayi.

Rashin yin bayanin gwamnatin jihar akan takamaiman inda mataimakin gwamnan yake ya haifar da bayyana mabanbantan ra’ayoyin al’umma da yan siyasa.

Haka zalika al’ummar Taraba sun nemi gwamna Agbu Kefas, yayi musu cikakken bayani akan inda aka kai mataimakin nasa.

Daily trust, tayi kokarin jin ta bakin kakakin majalisar dokokin jihar John Kizito, amma hakan bai samu ba, sakamakon yin tafiya zuwa kasashen ketare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here