Jami’an rundunar sojin kasa dake karkashin rukuni na uku, sun sanar da cewa sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 25, da bankaɗo lita dubu 95, na danyen man da aka sata a yankin Neja Delta.
Rundunar tace ta samu nasarar yin wannan aiki tare da hadin gwuiwar sauran jami’an tsaro.
Mataimakin daraktan yada labaran sojin Laftanar Kanar Jonah Danjuma, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar a birnin Fatakwal a karshen mako.
Yace sun yi atisayen ne a tsakanin ranakun 10 da 16 ga watan Fabrairu, da hakan yasa aka kama masu satar danyen mai su 12, da kama jiragen ruwa na satar man 18.