Malaman addini na neman kwace siyasa daga hannun yan siyasa—Sule Lamido

0
70

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, ya bayyana takaicin sa akan yadda yace malaman addini na neman kwace harkokin siyasa daga hannun yan siyasar.

Sule Lamido, ya bayyana hakan a jihar Kaduna, lokacin da yakai ziyarar ta’aziyya ga Sheikh Yusuf Sambo Rigacikum, sakamakon rasuwar babban É—ansa.

Tsohon gwamnan yace akwai damuwa akan yadda Malamai ke shigar da kansu cikin siyasa kace-kace, yana mai cewa a yanzu malamai suna taka rawa sosai a siyasance, da kuma jefa kuri’u a Najeriya.

Lamido, ya yiwa Malaman addinin shaguben cewa suna jira malaman su bayyana mutanen da suke zo a zaba.

Sule Lamido, ya kuma ce a yanayin da Najeriya ke ciki ya kamata kowa ya tsaya akan matsayin sa, da kuma bayyana gaskiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here