Akwai alamun cewa Kakakin majalisar dokokin jihar Lagos Mojisola Meranda, zata yi murabus daga mukamin ta a yau litinin, kamar yadda wata majiya ta bayyanawa jaridar Daily trust.
Fitar bayanin hakan yazo bayan da jami’an tsaron farin kaya DSS, suka mamaye zauren majalisar tare da rufe ofishin kakakin.
Wasu majiyoyi sunce jami’an sun mamaye majalisar dake Alausa a Ikeja, tun kafin yan majalisa su shiga domin gabatar da zaman su na yau litinin.
Majalisar dokokin jihar Lagos ta fada rikici tun bayan da aka tsige tsohon kakakin ta Mudashiru Obasa, wanda Obasa, yaki amincewa da tsigewar.
Akwai yiwuwar Obasa, ya cigaba da rike mukamin kakakin majalisar dokokin jihar Lagos, biyo bayan saka bakin shugaban kasa Tinubu akan rikicin.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa a yanzu haka Mojisola Meranda, na jagorantar zaman majalisar duk da cewa akwai jami’an tsaron.
Bayan haka zanga zanga ta barke a harabar majalisar dokokin jihar ta Lagos, yayin da ma’aikatan majalisar ke zaton ana shirya Makarkashiyar cire Meranda, daga mukamin ta.