Amurka zata koro yan Najeriya 201.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ne ya dauki aniyar korar baki daga kasar tun lokacin da yake yakin neman zabe.
Jakadan Amurka A Najeriya Richard Mills, ne ya sanar da hakan lokacin daya ziyarci karamar ministar harkokin waje Bianca Ojukwu, a gidan Tafawa Balewa dake Abuja.
:::An ƙone jami’an hukumar NDLEA da ransa a jihar Kaduna
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ta fitar tace wadanda za’a kwaso din za’a sauke su a filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe, dake birnin tarayya Abuja. Sannan cikin wadanda za’a koro akwai yan Najeriya da suka aikata lafuka ake tsare dasu a gidajen yarin Amurka.
Sauran wadanda za’a dawo dasu gida sun hadar mutanen da suka shiga Amurka ba bisa ka’ida ba.