Wasu mutane sun kashe jami’in hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta hanyar ƙone ƙurmus.
Lamarin ya faru a unguwar Gadan-Gayan dake karamar hukumar Igabi.
Sahara Reporters, ta rawaito cewa an kashe mutumin yayin da jami’an hukumar NDLEA suke kokarin kama wani mutum da ake zaton mai laifi ne.
Wanda jami’an ke kokarin kamawa an bayar da rahoton cewa dillalin miyagun kwayoyi ne, sannan ya kashe mutane uku a lokacin da yake kokarin tserewa jami’an da motar sa.
An bayyana cewa ma’aikacin NDLEA da aka kone ya gamu da fushin wasu matasa ne yayin da yake kokarin kwantar da rikicin daya barke bayan dillalin miyagun kwayoyin ya kashe mutane uku, inda matasan suka caccaka masa wuka, bayan an kai shi asibiti kuma suka je har can suka kone shi.
Iyalan mamacin sun zargi hukumar NDLEA da nuna rashin sanin ya kamata, bisa hujjar cewa har yanzu basu yi musu gaisuwar mutuwar jami’in, sannan basu bayar da wani cikakken bayani akan dalilin rasuwar tasa ba.
Kakakin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Femi Babafemi, ya tabbatar da kisan ma’aikacin nasu a bakin aiki.
Sai dai Femi Babafemi, ya musanta zargin iyalan mamacin.