Shugaba Tinubu ya nemi a bawa jami’ar Bayero filin unguwar Rimin Zakara

0
39

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya shiga tsakani a rikicin filaye tsakanin Jami’ar Bayero, (BUK) da al’ummar kauyen Rimin Zakara da ke makwabtaka da ita don ganin filin ya dawo hannun jami’ar.

 Shugaban ya sanar da hakan a jiya Asabar yayin bikin yaye daliban jami’ar karo na 39.

Tinubu, wanda karamar Ministan Harkokin Ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmed, ta wakilta, a taron yaye daliban ya bukaci gwamnan da ya shiga lamarin ta hanyar mayarwa da jami’ar takardun mallakar filin.

Ya kuma ce gwamnati na da masaniya kan kalubalen rashin shinge da jami’ar ke fuskanta, kuma ta samar da wasu kudade don gina shinge a kewayenta.

Shugaban kasar ya kuma bukaci jami’o’in kasar nan da su yi amfani da hanyoyin nazari da bincike don samar da hanyoyin samun wutar lantarki mai zaman kan ta domin rage kashe makudan kudade wajen samar da wuta a cikin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here