Ana zaton Jirgin Sojin Najeriya ya kashe mutane 10 a kauyen Zakka dake karamar hukumar Safana a jihar Katsina.
Kafar yada labarai ta DW Hausa, ta rawaito cewa lamarin ya faru a jiya Asabar a lokacin da sojojin Najeriya ke farautar ‘yan bindigar da suka kai hari a kauyen Zakka da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina.
Zuwa yanzu dai ba’a ji martanin rundunar sojin kasa dangane da batun kisan mutanen ba.
Wannan dai ba shine karon farko da ake samun kisan fararen hula daga jirgin yakin Sojin Najeriya ba, wanda hakan ya faru a jihohin Sokoto, Kaduna, Katsina da Zamfara.