Ana tsammanin wani wani Malami ya kashe budurwa don yin tsafi da ita

0
76

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wani malamin addini mai suna AbdulRahman Bello, da laifin kashe wata daliba domin yin tsafi da ita.

Marigayiyar mai suna Lawal Hafsoh Yetunde, an ce daliba ce dake shekarar karshe a kwalejin ilimi ta jihar Kwara, dake Ilọrin. 

An bayar da rahoton cewa ta bata a ranar 10 ga Fabrairu, 2025 bayan halartar bikin suna, inda aka ce wanda ake zargin ne ya kirawo ta a waya lokacin da take cin abinci.

Ana zaton mamaciyar ta hadu da Malamin a kafar sada zumunta ta Facebook.

Rundunar yan sandan jihar, ta tabbatar da kama wanda ake zargin ta bakin kakakin rundunar SP Adeoun Ejire.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here