Jakadan ƙasar Saudiyya a Birtaniya ya ce ƙasar sa ba za ta bari a sha giya ba a lokacin Gasar Cin Kofin Duniya ta 2034 da ƙasar za ta karɓi baƙunci.
A wata hira da manema labarai, Khalid Bin Bandar Al Saud, ya ce ba za su sauya daga al’adarsu ba sannan su karɓi ta wasu don kawai suna son karɓar baƙuncin wasan ƙwallon ƙafa.
A ranar 11 ga watan Disamba 2024, shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino, ya sanar da cewa an amince Saudiyya ta karbi bakuncin gasar kofin cin duniya a 2034.
Tun da farko gwamnatin kasar Saudi Arabia, ce ta nemi a bata damar karbar bakuncin gasar.