Rundunar yan sandan kasa tayi watsi da zargin batan bindigu 3,907 a hannun jami’an ta

0
45

Rundunar yan sandan Najeriya (NPF) tayi fatali da zargin cewa an nemi bindigu 3,907, an rasa daga hannun jami’an ta, inda tace zargin wasa da hankali ne kuma ba gaskiya bane.

Shalkwatar yan sanda ta bayyana hakan cikin wata sanarwar data fitar a yau Alhamis, inda tace an rasa makaman a sakamakon ayyukan rashin tsaro, da kuma lokutan da aka kaiwa jami’an yan sanda hari ko aka kashe su, sai kuma harin da ake kaiwa ma’ajiyar makamai.

Sannan sanarwar tace ana yin duk mai yiwuwa wajen kwato makaman da aka rasa.

:::Gwamnan jihar Kano ya bayyana jimamin sa akan rasuwar Dan Zago

Mai magana da yawun rundunar yan sandan kasa ACP Muyiwa Adejobi, yace tabbas suna yin kokarin kwato bindigun daga wajen wadanda suka sace su, wanda zuwa yanzu an samu nasarar bankado mutanen da suka kwace wasu daga cikin makaman, kuma an mayar dasu ma’ajiyar makamai ta rundunar yan sandan kasa.

Rundunar tace tayi mamakin samun zargin ta da cewa an rasa makamai 3,907 daga wajen jami’anta ta, inda ta jaddada cewa batun ba haka yake ba, kuma yan sanda basu karkatar da wadancan adadin makamai ba.

Idan za’a iya tunawa babban mai binciken kudi na gwamnatin tarayya ne ya sanar da rahoton cewa tun a shekarar 2019, an rasa wasu tarin makamai daga rundunar yan sandan, lamarin da ya haifar da rashin fahimta tsakanin yan sanda da mambobin majalisar dattawa masu kula da kwamitin asusun gwamnatin tarayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here