Majalisun dokokin kasa sun amince da karin da shugaban kasa Tinubu, ya nemi a yiwa kasafin kudin shekarar da muke ciki.
Majalisar tace a yanzu kasafin kudin 2025 zai tsaya akan naira triliyan 54.9.
Idan za’a iya tunawa a baya majalisar ta amince da kasafin naira triliyan 49.7, amma shugaban kasa Bola Tinubu, ya nemi a kara kasafin zuwa naira triliyan 54.2.
:::NNPCL ya rage farashin man fetur
Shugaban yace bukatar karin kasafin tazo a daidai lokacin da gwamnati ta gano wasu hanyoyin samun kudin shiga.
Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa Olamilekan Adeola, shine ya gabatar da rahoton amincewa karin kasafin, tare da takwaransa na Abubakar Bichi, na majalisar wakilai, tare da yin bayanin cewa kasafin zai tasamma naira triliyan 54.9.