Kotu ta dage sauraron shari’ar zargin Ganduje da Matar sa akan cin hanci da rashawa

0
49

Babbar kotun jihar Kano, ta dage sauraron shari’ar dake gabanta kan zargin cin hanci da rashawar da gwamnatin Kano ke yiwa tsohon gwamnan jihar Dr. A bdullahi Umar Ganduje da mai dakin sa Hafsat Ganduje, dangane da cin hanci da rashawa da karkatar da kudaden al’umma a lokacin mulkin sa.

Bayan Ganduje da matar sa, akwai karin wasu mutane 6, da ke cikin zargin.

:::An gudanar da jana’izar Dan Zago a fadar masarautar Kano

Kotun dai ta saka ranar 15, ga watan da muke ciki a matsayin lokacin cigaba da shari’ar har ma da sauraron duk wasu hujja akan wasu abubuwan da ba’a amince dasu ba yayin zaman shari’ar na baya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa gwamnatin Kano, tana zargin Ganduje da aikata wasu laifuka 8, da suka kunshi cin hanci da rashawa, almundahana, da sauran su.

Sauran da ake zargin Ganduje ya hada kai dasu wajen aikata almundahanar sun hadar da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash properties Limited,Safari Textiles Limited da sage General Enterprises Limited.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here