Kamfanin sadarwa na MTN ya janye karin farashin da yayi ga masu siyan Data 15GB.
Kamfanin ya sanar da hakan a shafin sa na X, a yau Alhamis.
:::An gudanar da jana’izar Dan Zago a fadar masarautar Kano
Da farko kamfanin yayi karin kaso 200 cikin dari ga masu siyan Data da takai 15GB.
A ranar Talatar data gabata ne kamfanin sadarwa na MTN, yayi karin kaso 200, cikin dari ga tsarin siyan data 15GB, zuwa sauran tsare-tsaren siyar Data.
Karin farashin ya haifar da rashin jin dadi ga masu hulda da kamfanin tsadar datar da suka tsinci kansu a ciki.