Kamfanin mai na NNPCL ya rage farashin litar fetur

0
127

Kamfanin mai na NNPCL ya sanar da rage farashin litar fetur daga 960 zuwa 945.

An samu raguwar farashin a yau alhamis bayan kamfanin ya umarci gidajen man sa, dasu yi kasa da farashin litar man.

Sai dai wasu daga cikin masu ababen hawa da aka zanta dasu sunce ragin bashi da wani alfanu bisa hujjar cewa hakan bazai kawo saukin rayuwa ba.

Kawo wannan lokaci wasu gidajen mai na yan kasuwa suna siyar da kowacce lita akan Naira 970 zuwa 960.

Shi kuwa kamfanin mai na MRS, ya sauko da nasa farashin litar man fetur zuwa Naira 925, a jihar Lagos, sannan a jihohin arewa MRS, yana siyar da litar man akan Naira 955.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here