Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta kama wani magatakarda na babbar kotu da mataimakinsa Sheriff mai ritaya, da lauyoyi uku da wasu 10 daga cikinsu jami’an tsaro bisa zarginsu da hannu a badakalar kudi sama da Naira biliyan 20.
SolaceBase ta ruwaito cewa shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin-Gado ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar.
Shugaban Hukumar ya yi karin haske kan yadda ake tafka barna a Kano, inda ya bayyana cewa ana taimaka wa haramtattun ayyuka a jihar.
Yace sun bankado wata kungiyar masu aikata laifuka da suka kware wajen kwace filayen jama’a.
Muhyi yace abin takaicin shi ne a cikin hadin gwiwar masu aikata laifin akwai lauyoyi, ma’aikatan kotuna, jami’an rajistar filaye, da jami’an tsaro.