Hukumar hana fasa kwauri ta kama bindigu da alburusai da aka shigo dasu Najeriya ta jihar Legas

0
62

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa Customs, ta kama wasu bindigu da alburusai masu yawa da aka shigo dasu Najeriya ba bisa ka’ida ba ta jihar Legas.

:::Gwamnatin Neja zata karya farashin Abinci saboda Azumin Ramadana

Duk da cewa ba’a kai ga bayyana adadin makaman da aka kama ba, amma akwai fargabar kalubalen tsaro ta fuskar yin fasa kwaurin makamai zuwa Najeriya, da a yanzu haka ke fama da matsalolin tsaron.

Shugaban hukumar hana fasa kwauri ta kasa Adewale Adeniyi, ya ziyarci jihar ta Lagos, don yiwa manema labarai karin haske akan yadda aka samu nasarar kama makaman da kuma abubuwan da aka samu.

Ana kyautata zaton bayanin nasa zai bayar da haske wajen bayyana daga inda makaman suka taho da kuma matakin da za’a dauka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here