An gudanar da jana’izar Alhaji Ahmadu Haruna Dan Zago, tsohon shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano.
An gudanar da jana’izar a Kofar Kudu, dake fadar mai martaba Sarkin Kano.
:::Kamfanin MTN ya janye karin kudin Data da yayi
Jana’izar ta samu halartar fitattun mutane da suka hadar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Dan Zago, ya rasu yana da shekaru 74, sannan ya bar Mata 4 da yaya 37 sai kuma jikoki da dama.
Bayan kammala jana’izar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya jagoranci zuwa gidan marigayin, domin yi musu ta’aziyyar rashin da suka yi.
Sauran wadanda suka je ta’aziyyar sun hadar da tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo da shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Ismail Jibrin Falgore sun shiga gidan marigayin inda suka yi da addu’oi domin nema masa gafarar Allah.