Shugaban hukumar tsaron farin kaya ta kasa SSS Oluwatosin Ajayi, yace akwai bukatar bawa wasu daga cikin yan Najeriya damar mallakar makamai domin kare kansu daga harin yan ta’adda.
Ajayi, yace hakan na daga cikin matakan dakile yaduwar ayyukan ta’addanci da rashin tsaro.
Shugaban ya sanar da hakan a yau lokacin daya halarci taron kungiyar AANISS na shekara shekara daya gudana a birnin tarayya Abuja.
Ajayi, ya bayar da misali da garin Azare na jihar Bauchi, inda mutane suka hada kai suka yaki yan ta’addan Boko Haram har suka yi nasara akan su.
Ya kuma ce ba abu ne mai yiwuwa ba ace sojoji da yan sanda zasu bawa kowanne dan kasa tsaron da ake bukata.