A ranar Talata data gabata ne kwamitin majalisar dattijai da ke kula da asusun kudin kasa, ya yi wa Sufeto Janar na ‘yan sandan kasa Kayode Egbetokun tambayoyi kan damuwar da ke tattare da bacewar bindigogi 178,459 da kuma zargi akan wata kwangilar Naira biliyan 1.1 da aka bawa rundunar ‘yan sanda.
A shekarar 2019 ne babban mai binciken kudi na kasa ya gabatarwa da majalisar dattawa rahoton cewa an samu bacewar bindugu 178,459 , mafi yawancin su kirar AK-47, a rundunar yan sandan kasa, wanda Samuel Godwin ya gabatar da rahoton a madadin Shaakaa Chira.
:::An saka ranar fara cinikin Pi Network a kasuwannin Crypto
A watan Disamba na shekarar 2018 an bayar da bayanin batan bindugu 178,459 , a cikin su guda 88,078, AK-47, ce, sannan a shekarar 2020, an samu bacewar kananun bindugu 3,907.
Haka ne yasa majalisar dattawan bayyana cewa makaman da aka siyo don kare rayuwar al’umma suna komawa hannun bata gari masu tayar da zaune tsaye.
Babban sufeton yan sandan Egbetokun, ya nemi afuwar majalisar bisa gaza bayyana a gaban ta lokacin da tayi masa wata gayyata, yana mai cewa ayyuka ne suka hana shi bayyana a majalisar.
Mataimakin babban sufeton yan sandan kasa, mai kula da asusun rundunar yan sandan AIG Abdul Sulaiman, ne ya wakilci Egbetokun, inda yace wasu makaman an rasa su lokacin fashi da makami yayin da aka rasa wasu lokacin da yan sanda suka fuskanci hari daga bata gari.
Yan majalisar dattawan dai sunce wannan batan bindugu shine ya ta’azzara ayyukan rashin tsaro a Najeriya.