Wadanda suka sace daraktan mulki na APC a matakin kasa sun nemi Naira miliyan 350

0
92

Masu garkuwa da mutanen da suka sace daraktan mulki na jam’iyyar APC, a matakin kasa DR. Raif Adeniji, sun nemi a biya su kudin fansa har naira miliyan 350, kafin su sake shi.

Masu garkuwar sun tuntubi iyalan Adeniji, inda suka ce tabbas sai an biya su wadancan makudan kudade, kamar yadda wani daga cikin iyalan mutumin ya sanar sannan ya nemi a sakaya sunan sa.

:::Yan fashi da yan ta’adda sun kwace bindugun yan sandan Najeriya guda 178,459

Jaridar Daily trust, ta rawaito cewa wata majiya daga cikin APC, ta sake tabbatar mata da hakan.

Wasu mutane ne dauke da muggan makami suka sace daraktan a yankin Kubwa dake karamar hukumar Bwari, a Abuja, wanda aka sace shi tare da dan uwan sa, sai matar sa dan uwan nasa, da kuma dansa. Sai dai an bayar da labarin mutuwar matar inda aka samu gawar ta a karamar Tafa dake jihar Niger.

Zuwa yanzu rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja bata ce komai ba akan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here