Manyan jagororin yan ta’adda sun mika wuya a jihar Katsina

0
90

Rahotanni sun bayyana cewa wasu manyan jagororin yan ta’addan da suka addabi kananun hukumomin Jibia da Safana a jihar Katsina, sun ajiye makamansu tare da mika wuya ga rundunar sojin kasa.

Mai bayar da rahoto akan ayyukan tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama, ya bayyana sunan manyan jagororin da suka hadar da Abu Radda, Umar Black, Abdullahi Lankai, da kuma Dabar Dan Gandu, wanda baki dayan su suke aikata ta’addanci a yankin karamar hukumar Jibia.

:::Dan majalisar wakilai ya sake ficewa daga PDP zuwa APC

Makama, yace mutanen sun mika wuya bayan da suka samu tsira daga wani harin sojoji, wanda tuni suka mika makaman su ga sojoji tare da sakin mutanen da suka yi garkuwa dasu.

Majiyar ta kara da cewa tsaffin mayakan sun roki gwamnati ta samar musu sana’ar da zasu dogara da kansu, bayan sun yi alkawarin rungumar zaman lafiya da kowa.

A litinin data gabata ne shalkwatar tsaron kasa tace tana shirin mayar da tsaffin mayakan Boko Haram cikin yan uwan su bayan an sauya musu tunani daga aikata ta’addanci zuwa zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here