Gwamnatin jihar Neja karkashin Mohammad Umar Bago, ta sha alwashin bayar da tallafi don saukaka farashin kayayyakin abinci albarkacin gabatowar watan azumin Ramadan.
:::Manyan jagororin yan ta’adda sun mika wuya a jihar Katsina
Sakataren yada labaran gwamnan Bologi Ibrahim, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar daya fitar inda yace gwamna Bago, ya sanar da haka ne a lokacin daya karbi bakuncin wakilan Gidauniyar Gate, bayan kai ziyara gidan gwamnatin ta Neja.
Bago, yace tabbas matakin da zasu dauki zai saukaka farashin abinci ga al’ummar Neja a yayin azumin.
Yace gwamnatin sa ta noma masara tan miliyan daya, kuma hakan zai daidaita farashin kayan abinci, sannan ya nemi taimakon gidauniyar Gates, wajen tallafawa mutane.
A nasa jawabin shugaban sashin ayyukan noma na gidauniyar Gates, Obai Khalifa ya ce tun kafuwar gidauniyar, a shekaru 25 da suka gabata, ta dauki alkawarin gina al’umma.