Babban turken wutar lantarkin Najeriya ya durkushe

0
86

Durkushwar babban turken wutar lantarkin kasa ya jefa al’umma da yawa cikin duhu.

Jaridar Punch, ta rawaito cewa turken lantarkin ya durkushe mintuna kadan bayan karfe 11 na safiyar yau Laraba.

:::Majalisar dattawa tayi barazanar kin amincewa da kasafin yan sanda na shekarar 2025

Kamfanin TCN, mai rarraba hasken lantarki ya tabbatar da lalacewar wutar cikin wani sakon daya fitar a shafin sa na X, wanda sanarwar tace lamarin ya faru da misalin karfe 11:34, na safiya.

Kamfanin yace injiniyoyin sa sun dukufa wajen ganin an gyara wutar tare da dawo da ita kamar yadda aka saba amfani da lantarkin a kowanne lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here