An saka ranar fara cinikin Pi Network a kasuwannin Crypto

0
101

Da alamu yan Baiwa sun kusa zama manyan masu Kudi.

Wasu daga cikin masana harkokin crypto a arewacin Najeriya sun bayyana cewa sun samu bayanin cewa babbar kasuwar Crypto ta OKX, zata yi listing din Pi a ranar 20 ga watan Fabrairu da muke ciki.

Haka zalika suma Pi sun bayyana hakan, inda suka rubuta Launching Open Mainnet February 20 2025, a cikin application din mining nasu da hakan ke tabbatar da yiwuwar kawo karshen dogon jiran da masu yin mining suka yi, na shafe kusan shekara 6, anayin mining din Pi, ba tare da fara kasuwancin sa ba.

An fara mining din Pi Network, a ranar 14 ga watan Maris a shekarar 2019, shekara 6 babu wata daya kenan.

Masana harkokin crypto dai na ganin cewa Pi Network, zai iya bayar da kudi masu yawa a lokacin daya shiga kasuwa yayin da wasu ke cewa sai bayan an dauki lokaci da shigar sa kasuwa zai bayar da kudi na mamaki.

Pi Network, dai shine mining na farko da ya kwashe shekaru masu yawa ba tare da shiga kasuwa ba, sannan mutane suna yi masa kyakyawan zato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here